Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

90 Al-Balad ٱلْبَلَد

< Previous   20 Āyah   The City      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

90:1 لَآ أُقْسِمُ بِهَـٰذَا ٱلْبَلَدِ
90:1 Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

90:2 وَأَنتَ حِلٌّۢ بِهَـٰذَا ٱلْبَلَدِ
90:2 Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari. - Abubakar Gumi (Hausa)

90:3 وَوَالِدٍ وَمَا وَلَدَ
90:3 Da mahaifi da abin da ya haifa. - Abubakar Gumi (Hausa)

90:4 لَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَـٰنَ فِى كَبَدٍ
90:4 Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala. - Abubakar Gumi (Hausa)

90:5 أَيَحْسَبُ أَن لَّن يَقْدِرَ عَلَيْهِ أَحَدٌ
90:5 Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa? - Abubakar Gumi (Hausa)

90:6 يَقُولُ أَهْلَكْتُ مَالًا لُّبَدًا
90:6 Yana cẽwa "Na halakarda dũkiya mai yawa," - Abubakar Gumi (Hausa)

90:7 أَيَحْسَبُ أَن لَّمْ يَرَهُۥٓ أَحَدٌ
90:7 Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

90:8 أَلَمْ نَجْعَل لَّهُۥ عَيْنَيْنِ
90:8 Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

90:9 وَلِسَانًا وَشَفَتَيْنِ
90:9 Da harshe, da leɓɓa biyu. - Abubakar Gumi (Hausa)

90:10 وَهَدَيْنَـٰهُ ٱلنَّجْدَيْنِ
90:10 Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi biyu ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

90:11 فَلَا ٱقْتَحَمَ ٱلْعَقَبَةَ
90:11 To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

90:12 وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْعَقَبَةُ
90:12 Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã? - Abubakar Gumi (Hausa)

90:13 فَكُّ رَقَبَةٍ
90:13 Ita ce fansar wuyan bãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

90:14 أَوْ إِطْعَـٰمٌ فِى يَوْمٍ ذِى مَسْغَبَةٍ
90:14 Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

90:15 يَتِيمًا ذَا مَقْرَبَةٍ
90:15 Ga marãya ma'abũcin zumunta. - Abubakar Gumi (Hausa)

90:16 أَوْ مِسْكِينًا ذَا مَتْرَبَةٍ
90:16 Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya. - Abubakar Gumi (Hausa)

90:17 ثُمَّ كَانَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَتَوَاصَوْا۟ بِٱلصَّبْرِ وَتَوَاصَوْا۟ بِٱلْمَرْحَمَةِ
90:17 Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi. - Abubakar Gumi (Hausa)

90:18 أُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلْمَيْمَنَةِ
90:18 Waɗannan ne ma'abũta albarka - Abubakar Gumi (Hausa)

90:19 وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا هُمْ أَصْحَـٰبُ ٱلْمَشْـَٔمَةِ
90:19 Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci - Abubakar Gumi (Hausa)

90:20 عَلَيْهِمْ نَارٌ مُّؤْصَدَةٌۢ
90:20 A kansu akwai wata wuta abar kullewa. - Abubakar Gumi (Hausa)