Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

70 Al-Ma`ārij ٱلْمَعَارِج

< Previous   44 Āyah   The Ascending Stairways      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

70:1 سَأَلَ سَآئِلٌۢ بِعَذَابٍ وَاقِعٍ
70:1 Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:2 لِّلْكَـٰفِرِينَ لَيْسَ لَهُۥ دَافِعٌ
70:2 Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:3 مِّنَ ٱللَّهِ ذِى ٱلْمَعَارِجِ
70:3 Daga Allah Mai matãkala. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:4 تَعْرُجُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ إِلَيْهِ فِى يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُۥ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ
70:4 Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:5 فَٱصْبِرْ صَبْرًا جَمِيلًا
70:5 Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:6 إِنَّهُمْ يَرَوْنَهُۥ بَعِيدًا
70:6 Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:7 وَنَرَىٰهُ قَرِيبًا
70:7 Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:8 يَوْمَ تَكُونُ ٱلسَّمَآءُ كَٱلْمُهْلِ
70:8 Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:9 وَتَكُونُ ٱلْجِبَالُ كَٱلْعِهْنِ
70:9 Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:10 وَلَا يَسْـَٔلُ حَمِيمٌ حَمِيمًا
70:10 Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:11 يُبَصَّرُونَهُمْ ۚ يَوَدُّ ٱلْمُجْرِمُ لَوْ يَفْتَدِى مِنْ عَذَابِ يَوْمِئِذٍۭ بِبَنِيهِ
70:11 Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa, - Abubakar Gumi (Hausa)

70:12 وَصَـٰحِبَتِهِۦ وَأَخِيهِ
70:12 Da matarsa da ɗan'uwansa. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:13 وَفَصِيلَتِهِ ٱلَّتِى تُـْٔوِيهِ
70:13 Da danginsa, mãsu tattarã shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:14 وَمَن فِى ٱلْأَرْضِ جَمِيعًا ثُمَّ يُنجِيهِ
70:14 Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:15 كَلَّآ ۖ إِنَّهَا لَظَىٰ
70:15 A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã, - Abubakar Gumi (Hausa)

70:16 نَزَّاعَةً لِّلشَّوَىٰ
70:16 Mai twãle fãtar goshi. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:17 تَدْعُوا۟ مَنْ أَدْبَرَ وَتَوَلَّىٰ
70:17 Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:18 وَجَمَعَ فَأَوْعَىٰٓ
70:18 Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:19 ۞ إِنَّ ٱلْإِنسَـٰنَ خُلِقَ هَلُوعًا
70:19 Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:20 إِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ جَزُوعًا
70:20 Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:21 وَإِذَا مَسَّهُ ٱلْخَيْرُ مَنُوعًا
70:21 Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:22 إِلَّا ٱلْمُصَلِّينَ
70:22 Sai mãsu yin salla, - Abubakar Gumi (Hausa)

70:23 ٱلَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ دَآئِمُونَ
70:23 Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:24 وَٱلَّذِينَ فِىٓ أَمْوَٰلِهِمْ حَقٌّ مَّعْلُومٌ
70:24 Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:25 لِّلسَّآئِلِ وَٱلْمَحْرُومِ
70:25 Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:26 وَٱلَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوْمِ ٱلدِّينِ
70:26 Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:27 وَٱلَّذِينَ هُم مِّنْ عَذَابِ رَبِّهِم مُّشْفِقُونَ
70:27 Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:28 إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمْ غَيْرُ مَأْمُونٍ
70:28 Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:29 وَٱلَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَـٰفِظُونَ
70:29 Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:30 إِلَّا عَلَىٰٓ أَزْوَٰجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَـٰنُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ
70:30 Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:31 فَمَنِ ٱبْتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْعَادُونَ
70:31 To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:32 وَٱلَّذِينَ هُمْ لِأَمَـٰنَـٰتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَٰعُونَ
70:32 Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:33 وَٱلَّذِينَ هُم بِشَهَـٰدَٰتِهِمْ قَآئِمُونَ
70:33 Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:34 وَٱلَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ
70:34 Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:35 أُو۟لَـٰٓئِكَ فِى جَنَّـٰتٍ مُّكْرَمُونَ
70:35 Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne - Abubakar Gumi (Hausa)

70:36 فَمَالِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ قِبَلَكَ مُهْطِعِينَ
70:36 Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu). - Abubakar Gumi (Hausa)

70:37 عَنِ ٱلْيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ عِزِينَ
70:37 Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a! - Abubakar Gumi (Hausa)

70:38 أَيَطْمَعُ كُلُّ ٱمْرِئٍ مِّنْهُمْ أَن يُدْخَلَ جَنَّةَ نَعِيمٍ
70:38 Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)? - Abubakar Gumi (Hausa)

70:39 كَلَّآ ۖ إِنَّا خَلَقْنَـٰهُم مِّمَّا يَعْلَمُونَ
70:39 A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:40 فَلَآ أُقْسِمُ بِرَبِّ ٱلْمَشَـٰرِقِ وَٱلْمَغَـٰرِبِ إِنَّا لَقَـٰدِرُونَ
70:40 Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:41 عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ خَيْرًا مِّنْهُمْ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ
70:41 Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:42 فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا۟ وَيَلْعَبُوا۟ حَتَّىٰ يُلَـٰقُوا۟ يَوْمَهُمُ ٱلَّذِى يُوعَدُونَ
70:42 Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita). - Abubakar Gumi (Hausa)

70:43 يَوْمَ يَخْرُجُونَ مِنَ ٱلْأَجْدَاثِ سِرَاعًا كَأَنَّهُمْ إِلَىٰ نُصُبٍ يُوفِضُونَ
70:43 Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

70:44 خَـٰشِعَةً أَبْصَـٰرُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ ۚ ذَٰلِكَ ٱلْيَوْمُ ٱلَّذِى كَانُوا۟ يُوعَدُونَ
70:44 Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.) - Abubakar Gumi (Hausa)