Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

26 Ash-Shu`arā' ٱلشُّعَرَاء

< Previous   227 Āyah   The Poets      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

26:1 طسٓمٓ
26:1 ¦. S̃. M̃. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:2 تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱلْكِتَـٰبِ ٱلْمُبِينِ
26:2 Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:3 لَعَلَّكَ بَـٰخِعٌ نَّفْسَكَ أَلَّا يَكُونُوا۟ مُؤْمِنِينَ
26:3 Tsammãninka kai mai halakar da ranka ne, dõmin ba su kasance mũminai ba! - Abubakar Gumi (Hausa)

26:4 إِن نَّشَأْ نُنَزِّلْ عَلَيْهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ ءَايَةً فَظَلَّتْ أَعْنَـٰقُهُمْ لَهَا خَـٰضِعِينَ
26:4 Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:5 وَمَا يَأْتِيهِم مِّن ذِكْرٍ مِّنَ ٱلرَّحْمَـٰنِ مُحْدَثٍ إِلَّا كَانُوا۟ عَنْهُ مُعْرِضِينَ
26:5 Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:6 فَقَدْ كَذَّبُوا۟ فَسَيَأْتِيهِمْ أَنۢبَـٰٓؤُا۟ مَا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ
26:6 To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:7 أَوَلَمْ يَرَوْا۟ إِلَى ٱلْأَرْضِ كَمْ أَنۢبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍ كَرِيمٍ
26:7 Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau? - Abubakar Gumi (Hausa)

26:8 إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
26:8 Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:9 وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
26:9 Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:10 وَإِذْ نَادَىٰ رَبُّكَ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱئْتِ ٱلْقَوْمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
26:10 Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:11 قَوْمَ فِرْعَوْنَ ۚ أَلَا يَتَّقُونَ
26:11 "Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:12 قَالَ رَبِّ إِنِّىٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ
26:12 Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:13 وَيَضِيقُ صَدْرِى وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِى فَأَرْسِلْ إِلَىٰ هَـٰرُونَ
26:13 "Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:14 وَلَهُمْ عَلَىَّ ذَنۢبٌ فَأَخَافُ أَن يَقْتُلُونِ
26:14 "Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:15 قَالَ كَلَّا ۖ فَٱذْهَبَا بِـَٔايَـٰتِنَآ ۖ إِنَّا مَعَكُم مُّسْتَمِعُونَ
26:15 Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:16 فَأْتِيَا فِرْعَوْنَ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولُ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
26:16 "Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:17 أَنْ أَرْسِلْ مَعَنَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ
26:17 "Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:18 قَالَ أَلَمْ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدًا وَلَبِثْتَ فِينَا مِنْ عُمُرِكَ سِنِينَ
26:18 Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:19 وَفَعَلْتَ فَعْلَتَكَ ٱلَّتِى فَعَلْتَ وَأَنتَ مِنَ ٱلْكَـٰفِرِينَ
26:19 "Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:20 قَالَ فَعَلْتُهَآ إِذًا وَأَنَا۠ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ
26:20 Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin hushi." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:21 فَفَرَرْتُ مِنكُمْ لَمَّا خِفْتُكُمْ فَوَهَبَ لِى رَبِّى حُكْمًا وَجَعَلَنِى مِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ
26:21 "Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:22 وَتِلْكَ نِعْمَةٌ تَمُنُّهَا عَلَىَّ أَنْ عَبَّدتَّ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ
26:22 "Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:23 قَالَ فِرْعَوْنُ وَمَا رَبُّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
26:23 Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:24 قَالَ رَبُّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَآ ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ
26:24 Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:25 قَالَ لِمَنْ حَوْلَهُۥٓ أَلَا تَسْتَمِعُونَ
26:25 Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:26 قَالَ رَبُّكُمْ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلْأَوَّلِينَ
26:26 Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:27 قَالَ إِنَّ رَسُولَكُمُ ٱلَّذِىٓ أُرْسِلَ إِلَيْكُمْ لَمَجْنُونٌ
26:27 Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:28 قَالَ رَبُّ ٱلْمَشْرِقِ وَٱلْمَغْرِبِ وَمَا بَيْنَهُمَآ ۖ إِن كُنتُمْ تَعْقِلُونَ
26:28 Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:29 قَالَ لَئِنِ ٱتَّخَذْتَ إِلَـٰهًا غَيْرِى لَأَجْعَلَنَّكَ مِنَ ٱلْمَسْجُونِينَ
26:29 Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:30 قَالَ أَوَلَوْ جِئْتُكَ بِشَىْءٍ مُّبِينٍ
26:30 Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:31 قَالَ فَأْتِ بِهِۦٓ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
26:31 Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:32 فَأَلْقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِىَ ثُعْبَانٌ مُّبِينٌ
26:32 Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:33 وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِىَ بَيْضَآءُ لِلنَّـٰظِرِينَ
26:33 Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:34 قَالَ لِلْمَلَإِ حَوْلَهُۥٓ إِنَّ هَـٰذَا لَسَـٰحِرٌ عَلِيمٌ
26:34 (Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi! - Abubakar Gumi (Hausa)

26:35 يُرِيدُ أَن يُخْرِجَكُم مِّنْ أَرْضِكُم بِسِحْرِهِۦ فَمَاذَا تَأْمُرُونَ
26:35 "Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:36 قَالُوٓا۟ أَرْجِهْ وَأَخَاهُ وَٱبْعَثْ فِى ٱلْمَدَآئِنِ حَـٰشِرِينَ
26:36 Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:37 يَأْتُوكَ بِكُلِّ سَحَّارٍ عَلِيمٍ
26:37 "Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:38 فَجُمِعَ ٱلسَّحَرَةُ لِمِيقَـٰتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ
26:38 Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:39 وَقِيلَ لِلنَّاسِ هَلْ أَنتُم مُّجْتَمِعُونَ
26:39 Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne? - Abubakar Gumi (Hausa)

26:40 لَعَلَّنَا نَتَّبِعُ ٱلسَّحَرَةَ إِن كَانُوا۟ هُمُ ٱلْغَـٰلِبِينَ
26:40 "Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:41 فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالُوا۟ لِفِرْعَوْنَ أَئِنَّ لَنَا لَأَجْرًا إِن كُنَّا نَحْنُ ٱلْغَـٰلِبِينَ
26:41 To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:42 قَالَ نَعَمْ وَإِنَّكُمْ إِذًا لَّمِنَ ٱلْمُقَرَّبِينَ
26:42 Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:43 قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلْقُوا۟ مَآ أَنتُم مُّلْقُونَ
26:43 Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:44 فَأَلْقَوْا۟ حِبَالَهُمْ وَعِصِيَّهُمْ وَقَالُوا۟ بِعِزَّةِ فِرْعَوْنَ إِنَّا لَنَحْنُ ٱلْغَـٰلِبُونَ
26:44 Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:45 فَأَلْقَىٰ مُوسَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِىَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ
26:45 Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:46 فَأُلْقِىَ ٱلسَّحَرَةُ سَـٰجِدِينَ
26:46 Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:47 قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
26:47 Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:48 رَبِّ مُوسَىٰ وَهَـٰرُونَ
26:48 "Ubangijin Mũsa da Hãrũna." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:49 قَالَ ءَامَنتُمْ لَهُۥ قَبْلَ أَنْ ءَاذَنَ لَكُمْ ۖ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِى عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحْرَ فَلَسَوْفَ تَعْلَمُونَ ۚ لَأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ وَأَرْجُلَكُم مِّنْ خِلَـٰفٍ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمْ أَجْمَعِينَ
26:49 Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:50 قَالُوا۟ لَا ضَيْرَ ۖ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ
26:50 Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:51 إِنَّا نَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لَنَا رَبُّنَا خَطَـٰيَـٰنَآ أَن كُنَّآ أَوَّلَ ٱلْمُؤْمِنِينَ
26:51 "Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:52 ۞ وَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنْ أَسْرِ بِعِبَادِىٓ إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
26:52 Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:53 فَأَرْسَلَ فِرْعَوْنُ فِى ٱلْمَدَآئِنِ حَـٰشِرِينَ
26:53 Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:54 إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَشِرْذِمَةٌ قَلِيلُونَ
26:54 "Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:55 وَإِنَّهُمْ لَنَا لَغَآئِظُونَ
26:55 "Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:56 وَإِنَّا لَجَمِيعٌ حَـٰذِرُونَ
26:56 "Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:57 فَأَخْرَجْنَـٰهُم مِّن جَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ
26:57 Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:58 وَكُنُوزٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ
26:58 Da taskõki da mazauni mai kyau. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:59 كَذَٰلِكَ وَأَوْرَثْنَـٰهَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ
26:59 Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:60 فَأَتْبَعُوهُم مُّشْرِقِينَ
26:60 Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:61 فَلَمَّا تَرَٰٓءَا ٱلْجَمْعَانِ قَالَ أَصْحَـٰبُ مُوسَىٰٓ إِنَّا لَمُدْرَكُونَ
26:61 Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:62 قَالَ كَلَّآ ۖ إِنَّ مَعِىَ رَبِّى سَيَهْدِينِ
26:62 Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:63 فَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱضْرِب بِّعَصَاكَ ٱلْبَحْرَ ۖ فَٱنفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرْقٍ كَٱلطَّوْدِ ٱلْعَظِيمِ
26:63 Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge, kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:64 وَأَزْلَفْنَا ثَمَّ ٱلْـَٔاخَرِينَ
26:64 Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:65 وَأَنجَيْنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓ أَجْمَعِينَ
26:65 Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:66 ثُمَّ أَغْرَقْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ
26:66 Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:67 إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
26:67 Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:68 وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
26:68 Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:69 وَٱتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ إِبْرَٰهِيمَ
26:69 Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:70 إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِۦ مَا تَعْبُدُونَ
26:70 A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:71 قَالُوا۟ نَعْبُدُ أَصْنَامًا فَنَظَلُّ لَهَا عَـٰكِفِينَ
26:71 Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:72 قَالَ هَلْ يَسْمَعُونَكُمْ إِذْ تَدْعُونَ
26:72 Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:73 أَوْ يَنفَعُونَكُمْ أَوْ يَضُرُّونَ
26:73 "Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:74 قَالُوا۟ بَلْ وَجَدْنَآ ءَابَآءَنَا كَذَٰلِكَ يَفْعَلُونَ
26:74 Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:75 قَالَ أَفَرَءَيْتُم مَّا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ
26:75 Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:76 أَنتُمْ وَءَابَآؤُكُمُ ٱلْأَقْدَمُونَ
26:76 "Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:77 فَإِنَّهُمْ عَدُوٌّ لِّىٓ إِلَّا رَبَّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
26:77 "To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:78 ٱلَّذِى خَلَقَنِى فَهُوَ يَهْدِينِ
26:78 "Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:79 وَٱلَّذِى هُوَ يُطْعِمُنِى وَيَسْقِينِ
26:79 "Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:80 وَإِذَا مَرِضْتُ فَهُوَ يَشْفِينِ
26:80 "Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:81 وَٱلَّذِى يُمِيتُنِى ثُمَّ يُحْيِينِ
26:81 "Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:82 وَٱلَّذِىٓ أَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لِى خَطِيٓـَٔتِى يَوْمَ ٱلدِّينِ
26:82 "Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:83 رَبِّ هَبْ لِى حُكْمًا وَأَلْحِقْنِى بِٱلصَّـٰلِحِينَ
26:83 "Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:84 وَٱجْعَل لِّى لِسَانَ صِدْقٍ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ
26:84 "Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya a cikin mutãnen ƙarshe." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:85 وَٱجْعَلْنِى مِن وَرَثَةِ جَنَّةِ ٱلنَّعِيمِ
26:85 "Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:86 وَٱغْفِرْ لِأَبِىٓ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ
26:86 "Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:87 وَلَا تُخْزِنِى يَوْمَ يُبْعَثُونَ
26:87 "Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:88 يَوْمَ لَا يَنفَعُ مَالٌ وَلَا بَنُونَ
26:88 "A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:89 إِلَّا مَنْ أَتَى ٱللَّهَ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ
26:89 "Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:90 وَأُزْلِفَتِ ٱلْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ
26:90 Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:91 وَبُرِّزَتِ ٱلْجَحِيمُ لِلْغَاوِينَ
26:91 Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:92 وَقِيلَ لَهُمْ أَيْنَ مَا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ
26:92 Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:93 مِن دُونِ ٱللَّهِ هَلْ يَنصُرُونَكُمْ أَوْ يَنتَصِرُونَ
26:93 "Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:94 فَكُبْكِبُوا۟ فِيهَا هُمْ وَٱلْغَاوُۥنَ
26:94 Sai aka kikkife su a cikinta, su da halakakkun. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:95 وَجُنُودُ إِبْلِيسَ أَجْمَعُونَ
26:95 Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:96 قَالُوا۟ وَهُمْ فِيهَا يَخْتَصِمُونَ
26:96 Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma, - Abubakar Gumi (Hausa)

26:97 تَٱللَّهِ إِن كُنَّا لَفِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ
26:97 "Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:98 إِذْ نُسَوِّيكُم بِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
26:98 "A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:99 وَمَآ أَضَلَّنَآ إِلَّا ٱلْمُجْرِمُونَ
26:99 "Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:100 فَمَا لَنَا مِن شَـٰفِعِينَ
26:100 "Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:101 وَلَا صَدِيقٍ حَمِيمٍ
26:101 "Kuma bã mu da abõki, masõyi." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:102 فَلَوْ أَنَّ لَنَا كَرَّةً فَنَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ
26:102 "Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:103 إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
26:103 Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:104 وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
26:104 Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:105 كَذَّبَتْ قَوْمُ نُوحٍ ٱلْمُرْسَلِينَ
26:105 Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:106 إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ نُوحٌ أَلَا تَتَّقُونَ
26:106 A lõkacin da ɗan'uwansu, Nũhu, ya ce musu, "Shin, bã zã ku yi taƙawa ba?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:107 إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
26:107 "Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:108 فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
26:108 "To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:109 وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
26:109 "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:110 فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
26:110 "Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:111 ۞ قَالُوٓا۟ أَنُؤْمِنُ لَكَ وَٱتَّبَعَكَ ٱلْأَرْذَلُونَ
26:111 Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:112 قَالَ وَمَا عِلْمِى بِمَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ
26:112 Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:113 إِنْ حِسَابُهُمْ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّى ۖ لَوْ تَشْعُرُونَ
26:113 "Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:114 وَمَآ أَنَا۠ بِطَارِدِ ٱلْمُؤْمِنِينَ
26:114 "Ban zama mai kõre mũminai ba." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:115 إِنْ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٌ مُّبِينٌ
26:115 "Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:116 قَالُوا۟ لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَـٰنُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمَرْجُومِينَ
26:116 Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:117 قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوْمِى كَذَّبُونِ
26:117 Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:118 فَٱفْتَحْ بَيْنِى وَبَيْنَهُمْ فَتْحًا وَنَجِّنِى وَمَن مَّعِىَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ
26:118 "Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:119 فَأَنجَيْنَـٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِى ٱلْفُلْكِ ٱلْمَشْحُونِ
26:119 Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:120 ثُمَّ أَغْرَقْنَا بَعْدُ ٱلْبَاقِينَ
26:120 Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:121 إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
26:121 Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:122 وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
26:122 Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:123 كَذَّبَتْ عَادٌ ٱلْمُرْسَلِينَ
26:123 Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:124 إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَ
26:124 A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:125 إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
26:125 "Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:126 فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
26:126 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:127 وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
26:127 "Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:128 أَتَبْنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ ءَايَةً تَعْبَثُونَ
26:128 "Shin, kunã yin ginin sitadiyo a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:129 وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمْ تَخْلُدُونَ
26:129 "Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:130 وَإِذَا بَطَشْتُم بَطَشْتُمْ جَبَّارِينَ
26:130 "Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:131 فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
26:131 "To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:132 وَٱتَّقُوا۟ ٱلَّذِىٓ أَمَدَّكُم بِمَا تَعْلَمُونَ
26:132 "Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:133 أَمَدَّكُم بِأَنْعَـٰمٍ وَبَنِينَ
26:133 "Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:134 وَجَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ
26:134 "Da gõnaki da marẽmari." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:135 إِنِّىٓ أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ
26:135 "Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:136 قَالُوا۟ سَوَآءٌ عَلَيْنَآ أَوَعَظْتَ أَمْ لَمْ تَكُن مِّنَ ٱلْوَٰعِظِينَ
26:136 Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:137 إِنْ هَـٰذَآ إِلَّا خُلُقُ ٱلْأَوَّلِينَ
26:137 "Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen mutãnen farko." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:138 وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ
26:138 "Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:139 فَكَذَّبُوهُ فَأَهْلَكْنَـٰهُمْ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
26:139 Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:140 وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
26:140 Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:141 كَذَّبَتْ ثَمُودُ ٱلْمُرْسَلِينَ
26:141 Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:142 إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ صَـٰلِحٌ أَلَا تَتَّقُونَ
26:142 A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:143 إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
26:143 "Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:144 فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
26:144 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:145 وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
26:145 "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:146 أَتُتْرَكُونَ فِى مَا هَـٰهُنَآ ءَامِنِينَ
26:146 "Shin, anã barin ku a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:147 فِى جَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ
26:147 "A cikin gõnaki da marẽmari." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:148 وَزُرُوعٍ وَنَخْلٍ طَلْعُهَا هَضِيمٌ
26:148 "Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi mãsu narkẽwa a ciki?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:149 وَتَنْحِتُونَ مِنَ ٱلْجِبَالِ بُيُوتًا فَـٰرِهِينَ
26:149 "Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:150 فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
26:150 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:151 وَلَا تُطِيعُوٓا۟ أَمْرَ ٱلْمُسْرِفِينَ
26:151 "Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:152 ٱلَّذِينَ يُفْسِدُونَ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا يُصْلِحُونَ
26:152 "Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:153 قَالُوٓا۟ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلْمُسَحَّرِينَ
26:153 Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:154 مَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُنَا فَأْتِ بِـَٔايَةٍ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
26:154 "Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:155 قَالَ هَـٰذِهِۦ نَاقَةٌ لَّهَا شِرْبٌ وَلَكُمْ شِرْبُ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ
26:155 Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan yini, kuma kunã da shan yini sasanne." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:156 وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٍ فَيَأْخُذَكُمْ عَذَابُ يَوْمٍ عَظِيمٍ
26:156 "Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:157 فَعَقَرُوهَا فَأَصْبَحُوا۟ نَـٰدِمِينَ
26:157 Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:158 فَأَخَذَهُمُ ٱلْعَذَابُ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
26:158 Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:159 وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
26:159 Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:160 كَذَّبَتْ قَوْمُ لُوطٍ ٱلْمُرْسَلِينَ
26:160 Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:161 إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ لُوطٌ أَلَا تَتَّقُونَ
26:161 A lõkacin da ɗan'uwansu, Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:162 إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
26:162 "Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:163 فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
26:163 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:164 وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
26:164 "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:165 أَتَأْتُونَ ٱلذُّكْرَانَ مِنَ ٱلْعَـٰلَمِينَ
26:165 "Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:166 وَتَذَرُونَ مَا خَلَقَ لَكُمْ رَبُّكُم مِّنْ أَزْوَٰجِكُم ۚ بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ عَادُونَ
26:166 "Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:167 قَالُوا۟ لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَـٰلُوطُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُخْرَجِينَ
26:167 Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:168 قَالَ إِنِّى لِعَمَلِكُم مِّنَ ٱلْقَالِينَ
26:168 Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:169 رَبِّ نَجِّنِى وَأَهْلِى مِمَّا يَعْمَلُونَ
26:169 "Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:170 فَنَجَّيْنَـٰهُ وَأَهْلَهُۥٓ أَجْمَعِينَ
26:170 Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:171 إِلَّا عَجُوزًا فِى ٱلْغَـٰبِرِينَ
26:171 Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:172 ثُمَّ دَمَّرْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ
26:172 Sa'an nan kuma Muka darkãke wasu. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:173 وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِم مَّطَرًا ۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلْمُنذَرِينَ
26:173 Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:174 إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
26:174 Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:175 وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
26:175 Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:176 كَذَّبَ أَصْحَـٰبُ لْـَٔيْكَةِ ٱلْمُرْسَلِينَ
26:176 Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:177 إِذْ قَالَ لَهُمْ شُعَيْبٌ أَلَا تَتَّقُونَ
26:177 A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:178 إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
26:178 "Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:179 فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
26:179 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:180 وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
26:180 "Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:181 ۞ أَوْفُوا۟ ٱلْكَيْلَ وَلَا تَكُونُوا۟ مِنَ ٱلْمُخْسِرِينَ
26:181 "Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:182 وَزِنُوا۟ بِٱلْقِسْطَاسِ ٱلْمُسْتَقِيمِ
26:182 "Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:183 وَلَا تَبْخَسُوا۟ ٱلنَّاسَ أَشْيَآءَهُمْ وَلَا تَعْثَوْا۟ فِى ٱلْأَرْضِ مُفْسِدِينَ
26:183 "Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:184 وَٱتَّقُوا۟ ٱلَّذِى خَلَقَكُمْ وَٱلْجِبِلَّةَ ٱلْأَوَّلِينَ
26:184 "Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:185 قَالُوٓا۟ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلْمُسَحَّرِينَ
26:185 Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:186 وَمَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُنَا وَإِن نَّظُنُّكَ لَمِنَ ٱلْكَـٰذِبِينَ
26:186 "Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:187 فَأَسْقِطْ عَلَيْنَا كِسَفًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
26:187 "To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:188 قَالَ رَبِّىٓ أَعْلَمُ بِمَا تَعْمَلُونَ
26:188 Ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:189 فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمْ عَذَابُ يَوْمِ ٱلظُّلَّةِ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ
26:189 Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:190 إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
26:190 Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:191 وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
26:191 Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:192 وَإِنَّهُۥ لَتَنزِيلُ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
26:192 Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:193 نَزَلَ بِهِ ٱلرُّوحُ ٱلْأَمِينُ
26:193 Rũhi amintacce ne ya sauka da shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:194 عَلَىٰ قَلْبِكَ لِتَكُونَ مِنَ ٱلْمُنذِرِينَ
26:194 A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:195 بِلِسَانٍ عَرَبِىٍّ مُّبِينٍ
26:195 Da harshe na Larabci mai bayãni. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:196 وَإِنَّهُۥ لَفِى زُبُرِ ٱلْأَوَّلِينَ
26:196 Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:197 أَوَلَمْ يَكُن لَّهُمْ ءَايَةً أَن يَعْلَمَهُۥ عُلَمَـٰٓؤُا۟ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ
26:197 Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi? - Abubakar Gumi (Hausa)

26:198 وَلَوْ نَزَّلْنَـٰهُ عَلَىٰ بَعْضِ ٱلْأَعْجَمِينَ
26:198 Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa, - Abubakar Gumi (Hausa)

26:199 فَقَرَأَهُۥ عَلَيْهِم مَّا كَانُوا۟ بِهِۦ مُؤْمِنِينَ
26:199 Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:200 كَذَٰلِكَ سَلَكْنَـٰهُ فِى قُلُوبِ ٱلْمُجْرِمِينَ
26:200 Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:201 لَا يُؤْمِنُونَ بِهِۦ حَتَّىٰ يَرَوُا۟ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَلِيمَ
26:201 Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:202 فَيَأْتِيَهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
26:202 Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:203 فَيَقُولُوا۟ هَلْ نَحْنُ مُنظَرُونَ
26:203 Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne?" - Abubakar Gumi (Hausa)

26:204 أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ
26:204 Ashe, to, da azãbarMu suke nẽman gaggãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

26:205 أَفَرَءَيْتَ إِن مَّتَّعْنَـٰهُمْ سِنِينَ
26:205 Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru, - Abubakar Gumi (Hausa)

26:206 ثُمَّ جَآءَهُم مَّا كَانُوا۟ يُوعَدُونَ
26:206 Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu, - Abubakar Gumi (Hausa)

26:207 مَآ أَغْنَىٰ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يُمَتَّعُونَ
26:207 Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare su. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:208 وَمَآ أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍ إِلَّا لَهَا مُنذِرُونَ
26:208 Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:209 ذِكْرَىٰ وَمَا كُنَّا ظَـٰلِمِينَ
26:209 Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:210 وَمَا تَنَزَّلَتْ بِهِ ٱلشَّيَـٰطِينُ
26:210 Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:211 وَمَا يَنۢبَغِى لَهُمْ وَمَا يَسْتَطِيعُونَ
26:211 Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:212 إِنَّهُمْ عَنِ ٱلسَّمْعِ لَمَعْزُولُونَ
26:212 Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:213 فَلَا تَدْعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ فَتَكُونَ مِنَ ٱلْمُعَذَّبِينَ
26:213 Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:214 وَأَنذِرْ عَشِيرَتَكَ ٱلْأَقْرَبِينَ
26:214 Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:215 وَٱخْفِضْ جَنَاحَكَ لِمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ
26:215 Kuma ka sassauta fikãfikanka ga wanda ya bĩ ka daga mũminai. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:216 فَإِنْ عَصَوْكَ فَقُلْ إِنِّى بَرِىٓءٌ مِّمَّا تَعْمَلُونَ
26:216 Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

26:217 وَتَوَكَّلْ عَلَى ٱلْعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ
26:217 Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:218 ٱلَّذِى يَرَىٰكَ حِينَ تَقُومُ
26:218 Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:219 وَتَقَلُّبَكَ فِى ٱلسَّـٰجِدِينَ
26:219 Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:220 إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ
26:220 Lalle Shi, Shi ne Mai ji, Masani. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:221 هَلْ أُنَبِّئُكُمْ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَـٰطِينُ
26:221 Shin, (kunã so) in gaya muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka? - Abubakar Gumi (Hausa)

26:222 تَنَزَّلُ عَلَىٰ كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ
26:222 Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:223 يُلْقُونَ ٱلسَّمْعَ وَأَكْثَرُهُمْ كَـٰذِبُونَ
26:223 Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:224 وَٱلشُّعَرَآءُ يَتَّبِعُهُمُ ٱلْغَاوُۥنَ
26:224 Kuma mawãƙa halakakku ne ke bin su. - Abubakar Gumi (Hausa)

26:225 أَلَمْ تَرَ أَنَّهُمْ فِى كُلِّ وَادٍ يَهِيمُونَ
26:225 Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

26:226 وَأَنَّهُمْ يَقُولُونَ مَا لَا يَفْعَلُونَ
26:226 Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

26:227 إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَذَكَرُوا۟ ٱللَّهَ كَثِيرًا وَٱنتَصَرُوا۟ مِنۢ بَعْدِ مَا ظُلِمُوا۟ ۗ وَسَيَعْلَمُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓا۟ أَىَّ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُونَ
26:227 Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)