Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

83 Al-Muţaffifīn ٱلْمُطَفِّفِين

< Previous   36 Āyah   The Defrauding      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

83:1 وَيْلٌ لِّلْمُطَفِّفِينَ
83:1 Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:2 ٱلَّذِينَ إِذَا ٱكْتَالُوا۟ عَلَى ٱلنَّاسِ يَسْتَوْفُونَ
83:2 Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:3 وَإِذَا كَالُوهُمْ أَو وَّزَنُوهُمْ يُخْسِرُونَ
83:3 Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa - Abubakar Gumi (Hausa)

83:4 أَلَا يَظُنُّ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَنَّهُم مَّبْعُوثُونَ
83:4 Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

83:5 لِيَوْمٍ عَظِيمٍ
83:5 Domin yini mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:6 يَوْمَ يَقُومُ ٱلنَّاسُ لِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
83:6 Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta? - Abubakar Gumi (Hausa)

83:7 كَلَّآ إِنَّ كِتَـٰبَ ٱلْفُجَّارِ لَفِى سِجِّينٍ
83:7 Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:8 وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا سِجِّينٌ
83:8 Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn? - Abubakar Gumi (Hausa)

83:9 كِتَـٰبٌ مَّرْقُومٌ
83:9 Wani 1ittãfi ne rubũtacce. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:10 وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
83:10 Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:11 ٱلَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوْمِ ٱلدِّينِ
83:11 Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:12 وَمَا يُكَذِّبُ بِهِۦٓ إِلَّا كُلُّ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ
83:12 Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:13 إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ ءَايَـٰتُنَا قَالَ أَسَـٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ
83:13 Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:14 كَلَّا ۖ بَلْ ۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ
83:14 A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:15 كَلَّآ إِنَّهُمْ عَن رَّبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّمَحْجُوبُونَ
83:15 A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:16 ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُوا۟ ٱلْجَحِيمِ
83:16 Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:17 ثُمَّ يُقَالُ هَـٰذَا ٱلَّذِى كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
83:17 Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi." - Abubakar Gumi (Hausa)

83:18 كَلَّآ إِنَّ كِتَـٰبَ ٱلْأَبْرَارِ لَفِى عِلِّيِّينَ
83:18 A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna? - Abubakar Gumi (Hausa)

83:19 وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا عِلِّيُّونَ
83:19 Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna? - Abubakar Gumi (Hausa)

83:20 كِتَـٰبٌ مَّرْقُومٌ
83:20 Wani littãfi ne rubũtacce. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:21 يَشْهَدُهُ ٱلْمُقَرَّبُونَ
83:21 Muƙarrabai suke halarta shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:22 إِنَّ ٱلْأَبْرَارَ لَفِى نَعِيمٍ
83:22 Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:23 عَلَى ٱلْأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ
83:23 A kan karagu, suna ta kallo. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:24 تَعْرِفُ فِى وُجُوهِهِمْ نَضْرَةَ ٱلنَّعِيمِ
83:24 Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:25 يُسْقَوْنَ مِن رَّحِيقٍ مَّخْتُومٍ
83:25 Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:26 خِتَـٰمُهُۥ مِسْكٌ ۚ وَفِى ذَٰلِكَ فَلْيَتَنَافَسِ ٱلْمُتَنَـٰفِسُونَ
83:26 ¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:27 وَمِزَاجُهُۥ مِن تَسْنِيمٍ
83:27 Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:28 عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا ٱلْمُقَرَّبُونَ
83:28 (Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:29 إِنَّ ٱلَّذِينَ أَجْرَمُوا۟ كَانُوا۟ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ يَضْحَكُونَ
83:29 Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:30 وَإِذَا مَرُّوا۟ بِهِمْ يَتَغَامَزُونَ
83:30 Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:31 وَإِذَا ٱنقَلَبُوٓا۟ إِلَىٰٓ أَهْلِهِمُ ٱنقَلَبُوا۟ فَكِهِينَ
83:31 Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:32 وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوٓا۟ إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَضَآلُّونَ
83:32 Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

83:33 وَمَآ أُرْسِلُوا۟ عَلَيْهِمْ حَـٰفِظِينَ
83:33 Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:34 فَٱلْيَوْمَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مِنَ ٱلْكُفَّارِ يَضْحَكُونَ
83:34 To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:35 عَلَى ٱلْأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ
83:35 A kan karagu, suna ta kallo. - Abubakar Gumi (Hausa)

83:36 هَلْ ثُوِّبَ ٱلْكُفَّارُ مَا كَانُوا۟ يَفْعَلُونَ
83:36 Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa? - Abubakar Gumi (Hausa)