Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

44 Ad-Dukhān ٱلدُّخَان

< Previous   59 Āyah   The Smoke      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

44:1 حمٓ
44:1 Ḥ. M̃. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:2 وَٱلْكِتَـٰبِ ٱلْمُبِينِ
44:2 Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:3 إِنَّآ أَنزَلْنَـٰهُ فِى لَيْلَةٍ مُّبَـٰرَكَةٍ ۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ
44:3 Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:4 فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ
44:4 A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:5 أَمْرًا مِّنْ عِندِنَآ ۚ إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ
44:5 Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:6 رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ
44:6 Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:7 رَبِّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَآ ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ
44:7 (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka). - Abubakar Gumi (Hausa)

44:8 لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْىِۦ وَيُمِيتُ ۖ رَبُّكُمْ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلْأَوَّلِينَ
44:8 Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:9 بَلْ هُمْ فِى شَكٍّ يَلْعَبُونَ
44:9 A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:10 فَٱرْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِى ٱلسَّمَآءُ بِدُخَانٍ مُّبِينٍ
44:10 Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:11 يَغْشَى ٱلنَّاسَ ۖ هَـٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٌ
44:11 Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:12 رَّبَّنَا ٱكْشِفْ عَنَّا ٱلْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ
44:12 Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:13 أَنَّىٰ لَهُمُ ٱلذِّكْرَىٰ وَقَدْ جَآءَهُمْ رَسُولٌ مُّبِينٌ
44:13 Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)? - Abubakar Gumi (Hausa)

44:14 ثُمَّ تَوَلَّوْا۟ عَنْهُ وَقَالُوا۟ مُعَلَّمٌ مَّجْنُونٌ
44:14 Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci." - Abubakar Gumi (Hausa)

44:15 إِنَّا كَاشِفُوا۟ ٱلْعَذَابِ قَلِيلًا ۚ إِنَّكُمْ عَآئِدُونَ
44:15 Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin). - Abubakar Gumi (Hausa)

44:16 يَوْمَ نَبْطِشُ ٱلْبَطْشَةَ ٱلْكُبْرَىٰٓ إِنَّا مُنتَقِمُونَ
44:16 Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:17 ۞ وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَآءَهُمْ رَسُولٌ كَرِيمٌ
44:17 Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:18 أَنْ أَدُّوٓا۟ إِلَىَّ عِبَادَ ٱللَّهِ ۖ إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
44:18 (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku." - Abubakar Gumi (Hausa)

44:19 وَأَن لَّا تَعْلُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ ۖ إِنِّىٓ ءَاتِيكُم بِسُلْطَـٰنٍ مُّبِينٍ
44:19 "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne." - Abubakar Gumi (Hausa)

44:20 وَإِنِّى عُذْتُ بِرَبِّى وَرَبِّكُمْ أَن تَرْجُمُونِ
44:20 "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni." - Abubakar Gumi (Hausa)

44:21 وَإِن لَّمْ تُؤْمِنُوا۟ لِى فَٱعْتَزِلُونِ
44:21 "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni." - Abubakar Gumi (Hausa)

44:22 فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ قَوْمٌ مُّجْرِمُونَ
44:22 Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:23 فَأَسْرِ بِعِبَادِى لَيْلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
44:23 (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)" - Abubakar Gumi (Hausa)

44:24 وَٱتْرُكِ ٱلْبَحْرَ رَهْوًا ۖ إِنَّهُمْ جُندٌ مُّغْرَقُونَ
44:24 "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

44:25 كَمْ تَرَكُوا۟ مِن جَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ
44:25 Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:26 وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ
44:26 Da shuke-shuke da matsayi mai kyau. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:27 وَنَعْمَةٍ كَانُوا۟ فِيهَا فَـٰكِهِينَ
44:27 Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:28 كَذَٰلِكَ ۖ وَأَوْرَثْنَـٰهَا قَوْمًا ءَاخَرِينَ
44:28 Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:29 فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ ٱلسَّمَآءُ وَٱلْأَرْضُ وَمَا كَانُوا۟ مُنظَرِينَ
44:29 Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:30 وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ مِنَ ٱلْعَذَابِ ٱلْمُهِينِ
44:30 Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:31 مِن فِرْعَوْنَ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَالِيًا مِّنَ ٱلْمُسْرِفِينَ
44:31 Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:32 وَلَقَدِ ٱخْتَرْنَـٰهُمْ عَلَىٰ عِلْمٍ عَلَى ٱلْعَـٰلَمِينَ
44:32 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:33 وَءَاتَيْنَـٰهُم مِّنَ ٱلْـَٔايَـٰتِ مَا فِيهِ بَلَـٰٓؤٌا۟ مُّبِينٌ
44:33 Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna - Abubakar Gumi (Hausa)

44:34 إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَيَقُولُونَ
44:34 Lalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa, - Abubakar Gumi (Hausa)

44:35 إِنْ هِىَ إِلَّا مَوْتَتُنَا ٱلْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ
44:35 "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba." - Abubakar Gumi (Hausa)

44:36 فَأْتُوا۟ بِـَٔابَآئِنَآ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ
44:36 "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya." - Abubakar Gumi (Hausa)

44:37 أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّعٍ وَٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ أَهْلَكْنَـٰهُمْ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ مُجْرِمِينَ
44:37 shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:38 وَمَا خَلَقْنَا ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَـٰعِبِينَ
44:38 Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:39 مَا خَلَقْنَـٰهُمَآ إِلَّا بِٱلْحَقِّ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
44:39 Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:40 إِنَّ يَوْمَ ٱلْفَصْلِ مِيقَـٰتُهُمْ أَجْمَعِينَ
44:40 Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:41 يَوْمَ لَا يُغْنِى مَوْلًى عَن مَّوْلًى شَيْـًٔا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ
44:41 Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:42 إِلَّا مَن رَّحِمَ ٱللَّهُ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
44:42 fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:43 إِنَّ شَجَرَتَ ٱلزَّقُّومِ
44:43 Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã), - Abubakar Gumi (Hausa)

44:44 طَعَامُ ٱلْأَثِيمِ
44:44 Ita ce abincin mai laifi. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:45 كَٱلْمُهْلِ يَغْلِى فِى ٱلْبُطُونِ
44:45 Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:46 كَغَلْىِ ٱلْحَمِيمِ
44:46 Kamar tafasar ruwan zãfi. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:47 خُذُوهُ فَٱعْتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَآءِ ٱلْجَحِيمِ
44:47 (A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm." - Abubakar Gumi (Hausa)

44:48 ثُمَّ صُبُّوا۟ فَوْقَ رَأْسِهِۦ مِنْ عَذَابِ ٱلْحَمِيمِ
44:48 "Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi." - Abubakar Gumi (Hausa)

44:49 ذُقْ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْكَرِيمُ
44:49 (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!" - Abubakar Gumi (Hausa)

44:50 إِنَّ هَـٰذَا مَا كُنتُم بِهِۦ تَمْتَرُونَ
44:50 "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi." - Abubakar Gumi (Hausa)

44:51 إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى مَقَامٍ أَمِينٍ
44:51 Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:52 فِى جَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ
44:52 A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:53 يَلْبَسُونَ مِن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَقَـٰبِلِينَ
44:53 Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:54 كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَـٰهُم بِحُورٍ عِينٍ
44:54 Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:55 يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَـٰكِهَةٍ ءَامِنِينَ
44:55 Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro). - Abubakar Gumi (Hausa)

44:56 لَا يَذُوقُونَ فِيهَا ٱلْمَوْتَ إِلَّا ٱلْمَوْتَةَ ٱلْأُولَىٰ ۖ وَوَقَىٰهُمْ عَذَابَ ٱلْجَحِيمِ
44:56 Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:57 فَضْلًا مِّن رَّبِّكَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ
44:57 Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:58 فَإِنَّمَا يَسَّرْنَـٰهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
44:58 Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

44:59 فَٱرْتَقِبْ إِنَّهُم مُّرْتَقِبُونَ
44:59 Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne. - Abubakar Gumi (Hausa)