Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

79 An-Nāzi`āt ٱلنَّازِعَات

< Previous   46 Āyah   Those who drag forth      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

79:1 وَٱلنَّـٰزِعَـٰتِ غَرْقًا
79:1 Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:2 وَٱلنَّـٰشِطَـٰتِ نَشْطًا
79:2 Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:3 وَٱلسَّـٰبِحَـٰتِ سَبْحًا
79:3 Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:4 فَٱلسَّـٰبِقَـٰتِ سَبْقًا
79:4 Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:5 فَٱلْمُدَبِّرَٰتِ أَمْرًا
79:5 Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:6 يَوْمَ تَرْجُفُ ٱلرَّاجِفَةُ
79:6 Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:7 تَتْبَعُهَا ٱلرَّادِفَةُ
79:7 Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:8 قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ
79:8 Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:9 أَبْصَـٰرُهَا خَـٰشِعَةٌ
79:9 Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:10 يَقُولُونَ أَءِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِى ٱلْحَافِرَةِ
79:10 Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu? - Abubakar Gumi (Hausa)

79:11 أَءِذَا كُنَّا عِظَـٰمًا نَّخِرَةً
79:11 "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?" - Abubakar Gumi (Hausa)

79:12 قَالُوا۟ تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ
79:12 Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!" - Abubakar Gumi (Hausa)

79:13 فَإِنَّمَا هِىَ زَجْرَةٌ وَٰحِدَةٌ
79:13 To, ita kam, tsãwa guda kawai ce. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:14 فَإِذَا هُم بِٱلسَّاهِرَةِ
79:14 Sai kawai gã su a bãyan ƙasa. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:15 هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ
79:15 Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka? - Abubakar Gumi (Hausa)

79:16 إِذْ نَادَىٰهُ رَبُّهُۥ بِٱلْوَادِ ٱلْمُقَدَّسِ طُوًى
79:16 A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã? - Abubakar Gumi (Hausa)

79:17 ٱذْهَبْ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ
79:17 Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:18 فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَىٰٓ أَن تَزَكَّىٰ
79:18 "Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:19 وَأَهْدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخْشَىٰ
79:19 "Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?" - Abubakar Gumi (Hausa)

79:20 فَأَرَىٰهُ ٱلْـَٔايَةَ ٱلْكُبْرَىٰ
79:20 Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:21 فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ
79:21 Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni), - Abubakar Gumi (Hausa)

79:22 ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَىٰ
79:22 Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:23 فَحَشَرَ فَنَادَىٰ
79:23 Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:24 فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلْأَعْلَىٰ
79:24 Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka." - Abubakar Gumi (Hausa)

79:25 فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلْـَٔاخِرَةِ وَٱلْأُولَىٰٓ
79:25 Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:26 إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَىٰٓ
79:26 Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:27 ءَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ ٱلسَّمَآءُ ۚ بَنَىٰهَا
79:27 Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:28 رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّىٰهَا
79:28 Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:29 وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَىٰهَا
79:29 Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:30 وَٱلْأَرْضَ بَعْدَ ذَٰلِكَ دَحَىٰهَآ
79:30 Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:31 أَخْرَجَ مِنْهَا مَآءَهَا وَمَرْعَىٰهَا
79:31 Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:32 وَٱلْجِبَالَ أَرْسَىٰهَا
79:32 Da duwatsu, Yã kafe ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:33 مَتَـٰعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَـٰمِكُمْ
79:33 Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:34 فَإِذَا جَآءَتِ ٱلطَّآمَّةُ ٱلْكُبْرَىٰ
79:34 To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:35 يَوْمَ يَتَذَكَّرُ ٱلْإِنسَـٰنُ مَا سَعَىٰ
79:35 Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:36 وَبُرِّزَتِ ٱلْجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ
79:36 Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:37 فَأَمَّا مَن طَغَىٰ
79:37 To, amma wanda ya yi girman kai. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:38 وَءَاثَرَ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا
79:38 Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya). - Abubakar Gumi (Hausa)

79:39 فَإِنَّ ٱلْجَحِيمَ هِىَ ٱلْمَأْوَىٰ
79:39 To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:40 وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ وَنَهَى ٱلنَّفْسَ عَنِ ٱلْهَوَىٰ
79:40 Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:41 فَإِنَّ ٱلْجَنَّةَ هِىَ ٱلْمَأْوَىٰ
79:41 To, lalle ne Aljanna ita ce makõma. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:42 يَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَىٰهَا
79:42 Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta? - Abubakar Gumi (Hausa)

79:43 فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَىٰهَآ
79:43 Me ya haɗã ka da ambatonta? - Abubakar Gumi (Hausa)

79:44 إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَىٰهَآ
79:44 Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:45 إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَىٰهَا
79:45 Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

79:46 كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوٓا۟ إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَىٰهَا
79:46 Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa. - Abubakar Gumi (Hausa)