Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

56 Al-Wāqi`ah ٱلْوَاقِعَة

< Previous   96 Āyah   The Inevitable      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

56:1 إِذَا وَقَعَتِ ٱلْوَاقِعَةُ
56:1 Idan mai aukuwa ta auku. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:2 لَيْسَ لِوَقْعَتِهَا كَاذِبَةٌ
56:2 Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:3 خَافِضَةٌ رَّافِعَةٌ
56:3 (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:4 إِذَا رُجَّتِ ٱلْأَرْضُ رَجًّا
56:4 Idan aka girgiza ƙasã girgizwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:5 وَبُسَّتِ ٱلْجِبَالُ بَسًّا
56:5 Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:6 فَكَانَتْ هَبَآءً مُّنۢبَثًّا
56:6 Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:7 وَكُنتُمْ أَزْوَٰجًا ثَلَـٰثَةً
56:7 Kuma kun kasance nau'i uku. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:8 فَأَصْحَـٰبُ ٱلْمَيْمَنَةِ مَآ أَصْحَـٰبُ ٱلْمَيْمَنَةِ
56:8 Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:9 وَأَصْحَـٰبُ ٱلْمَشْـَٔمَةِ مَآ أَصْحَـٰبُ ٱلْمَشْـَٔمَةِ
56:9 Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:10 وَٱلسَّـٰبِقُونَ ٱلسَّـٰبِقُونَ
56:10 Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan, - Abubakar Gumi (Hausa)

56:11 أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلْمُقَرَّبُونَ
56:11 Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:12 فِى جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ
56:12 A ckin Aljannar ni'ima. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:13 ثُلَّةٌ مِّنَ ٱلْأَوَّلِينَ
56:13 Jama'a ne daga mutãnen farko. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:14 وَقَلِيلٌ مِّنَ ٱلْـَٔاخِرِينَ
56:14 Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:15 عَلَىٰ سُرُرٍ مَّوْضُونَةٍ
56:15 (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:16 مُّتَّكِـِٔينَ عَلَيْهَا مُتَقَـٰبِلِينَ
56:16 Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:17 يَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَٰنٌ مُّخَلَّدُونَ
56:17 Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:18 بِأَكْوَابٍ وَأَبَارِيقَ وَكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍ
56:18 Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:19 لَّا يُصَدَّعُونَ عَنْهَا وَلَا يُنزِفُونَ
56:19 Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:20 وَفَـٰكِهَةٍ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ
56:20 Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:21 وَلَحْمِ طَيْرٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ
56:21 Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:22 وَحُورٌ عِينٌ
56:22 Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:23 كَأَمْثَـٰلِ ٱللُّؤْلُؤِ ٱلْمَكْنُونِ
56:23 Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:24 جَزَآءًۢ بِمَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ
56:24 A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:25 لَا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا تَأْثِيمًا
56:25 Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:26 إِلَّا قِيلًا سَلَـٰمًا سَلَـٰمًا
56:26 Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:27 وَأَصْحَـٰبُ ٱلْيَمِينِ مَآ أَصْحَـٰبُ ٱلْيَمِينِ
56:27 Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:28 فِى سِدْرٍ مَّخْضُودٍ
56:28 (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:29 وَطَلْحٍ مَّنضُودٍ
56:29 Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:30 وَظِلٍّ مَّمْدُودٍ
56:30 Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:31 وَمَآءٍ مَّسْكُوبٍ
56:31 Da wani ruwa mai gudãna. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:32 وَفَـٰكِهَةٍ كَثِيرَةٍ
56:32 Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:33 لَّا مَقْطُوعَةٍ وَلَا مَمْنُوعَةٍ
56:33 Bã su yankẽwa kuma bã a hana su. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:34 وَفُرُشٍ مَّرْفُوعَةٍ
56:34 Da wasu shimfiɗu maɗaukaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:35 إِنَّآ أَنشَأْنَـٰهُنَّ إِنشَآءً
56:35 Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:36 فَجَعَلْنَـٰهُنَّ أَبْكَارًا
56:36 Sa'an nan Muka sanya su budurwai. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:37 عُرُبًا أَتْرَابًا
56:37 Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:38 لِّأَصْحَـٰبِ ٱلْيَمِينِ
56:38 Ga mazõwa dãma. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:39 ثُلَّةٌ مِّنَ ٱلْأَوَّلِينَ
56:39 Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:40 وَثُلَّةٌ مِّنَ ٱلْـَٔاخِرِينَ
56:40 Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:41 وَأَصْحَـٰبُ ٱلشِّمَالِ مَآ أَصْحَـٰبُ ٱلشِّمَالِ
56:41 Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:42 فِى سَمُومٍ وَحَمِيمٍ
56:42 Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:43 وَظِلٍّ مِّن يَحْمُومٍ
56:43 Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:44 لَّا بَارِدٍ وَلَا كَرِيمٍ
56:44 Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:45 إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَبْلَ ذَٰلِكَ مُتْرَفِينَ
56:45 Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:46 وَكَانُوا۟ يُصِرُّونَ عَلَى ٱلْحِنثِ ٱلْعَظِيمِ
56:46 Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:47 وَكَانُوا۟ يَقُولُونَ أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَـٰمًا أَءِنَّا لَمَبْعُوثُونَ
56:47 Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?" - Abubakar Gumi (Hausa)

56:48 أَوَءَابَآؤُنَا ٱلْأَوَّلُونَ
56:48 "Shin, kuma da ubanninmu na farko?" - Abubakar Gumi (Hausa)

56:49 قُلْ إِنَّ ٱلْأَوَّلِينَ وَٱلْـَٔاخِرِينَ
56:49 Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe." - Abubakar Gumi (Hausa)

56:50 لَمَجْمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَـٰتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ
56:50 "Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne." - Abubakar Gumi (Hausa)

56:51 ثُمَّ إِنَّكُمْ أَيُّهَا ٱلضَّآلُّونَ ٱلْمُكَذِّبُونَ
56:51 "Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!" - Abubakar Gumi (Hausa)

56:52 لَـَٔاكِلُونَ مِن شَجَرٍ مِّن زَقُّومٍ
56:52 "Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)." - Abubakar Gumi (Hausa)

56:53 فَمَالِـُٔونَ مِنْهَا ٱلْبُطُونَ
56:53 "Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta." - Abubakar Gumi (Hausa)

56:54 فَشَـٰرِبُونَ عَلَيْهِ مِنَ ٱلْحَمِيمِ
56:54 "Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi." - Abubakar Gumi (Hausa)

56:55 فَشَـٰرِبُونَ شُرْبَ ٱلْهِيمِ
56:55 "Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

56:56 هَـٰذَا نُزُلُهُمْ يَوْمَ ٱلدِّينِ
56:56 Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:57 نَحْنُ خَلَقْنَـٰكُمْ فَلَوْلَا تُصَدِّقُونَ
56:57 Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:58 أَفَرَءَيْتُم مَّا تُمْنُونَ
56:58 Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:59 ءَأَنتُمْ تَخْلُقُونَهُۥٓ أَمْ نَحْنُ ٱلْخَـٰلِقُونَ
56:59 Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:60 نَحْنُ قَدَّرْنَا بَيْنَكُمُ ٱلْمَوْتَ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ
56:60 Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba, - Abubakar Gumi (Hausa)

56:61 عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمْثَـٰلَكُمْ وَنُنشِئَكُمْ فِى مَا لَا تَعْلَمُونَ
56:61 A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:62 وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ ٱلنَّشْأَةَ ٱلْأُولَىٰ فَلَوْلَا تَذَكَّرُونَ
56:62 Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:63 أَفَرَءَيْتُم مَّا تَحْرُثُونَ
56:63 Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:64 ءَأَنتُمْ تَزْرَعُونَهُۥٓ أَمْ نَحْنُ ٱلزَّٰرِعُونَ
56:64 Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:65 لَوْ نَشَآءُ لَجَعَلْنَـٰهُ حُطَـٰمًا فَظَلْتُمْ تَفَكَّهُونَ
56:65 Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:66 إِنَّا لَمُغْرَمُونَ
56:66 (Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!" - Abubakar Gumi (Hausa)

56:67 بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ
56:67 "Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!" - Abubakar Gumi (Hausa)

56:68 أَفَرَءَيْتُمُ ٱلْمَآءَ ٱلَّذِى تَشْرَبُونَ
56:68 Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:69 ءَأَنتُمْ أَنزَلْتُمُوهُ مِنَ ٱلْمُزْنِ أَمْ نَحْنُ ٱلْمُنزِلُونَ
56:69 Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:70 لَوْ نَشَآءُ جَعَلْنَـٰهُ أُجَاجًا فَلَوْلَا تَشْكُرُونَ
56:70 Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:71 أَفَرَءَيْتُمُ ٱلنَّارَ ٱلَّتِى تُورُونَ
56:71 Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:72 ءَأَنتُمْ أَنشَأْتُمْ شَجَرَتَهَآ أَمْ نَحْنُ ٱلْمُنشِـُٔونَ
56:72 Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:73 نَحْنُ جَعَلْنَـٰهَا تَذْكِرَةً وَمَتَـٰعًا لِّلْمُقْوِينَ
56:73 Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:74 فَسَبِّحْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلْعَظِيمِ
56:74 Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:75 ۞ فَلَآ أُقْسِمُ بِمَوَٰقِعِ ٱلنُّجُومِ
56:75 To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:76 وَإِنَّهُۥ لَقَسَمٌ لَّوْ تَعْلَمُونَ عَظِيمٌ
56:76 Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:77 إِنَّهُۥ لَقُرْءَانٌ كَرِيمٌ
56:77 Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:78 فِى كِتَـٰبٍ مَّكْنُونٍ
56:78 A cikin wani littafi tsararre. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:79 لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلْمُطَهَّرُونَ
56:79 Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:80 تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
56:80 Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:81 أَفَبِهَـٰذَا ٱلْحَدِيثِ أَنتُم مُّدْهِنُونَ
56:81 Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:82 وَتَجْعَلُونَ رِزْقَكُمْ أَنَّكُمْ تُكَذِّبُونَ
56:82 Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:83 فَلَوْلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلْحُلْقُومَ
56:83 To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa). - Abubakar Gumi (Hausa)

56:84 وَأَنتُمْ حِينَئِذٍ تَنظُرُونَ
56:84 Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:85 وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنكُمْ وَلَـٰكِن لَّا تُبْصِرُونَ
56:85 Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:86 فَلَوْلَآ إِن كُنتُمْ غَيْرَ مَدِينِينَ
56:86 To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

56:87 تَرْجِعُونَهَآ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ
56:87 Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:88 فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلْمُقَرَّبِينَ
56:88 To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta, - Abubakar Gumi (Hausa)

56:89 فَرَوْحٌ وَرَيْحَانٌ وَجَنَّتُ نَعِيمٍ
56:89 Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:90 وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنْ أَصْحَـٰبِ ٱلْيَمِينِ
56:90 Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma, - Abubakar Gumi (Hausa)

56:91 فَسَلَـٰمٌ لَّكَ مِنْ أَصْحَـٰبِ ٱلْيَمِينِ
56:91 Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:92 وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلْمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ
56:92 Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun, - Abubakar Gumi (Hausa)

56:93 فَنُزُلٌ مِّنْ حَمِيمٍ
56:93 Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:94 وَتَصْلِيَةُ جَحِيمٍ
56:94 Da ƙõnuwa da Jahĩm, - Abubakar Gumi (Hausa)

56:95 إِنَّ هَـٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلْيَقِينِ
56:95 Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni. - Abubakar Gumi (Hausa)

56:96 فَسَبِّحْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلْعَظِيمِ
56:96 Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci. - Abubakar Gumi (Hausa)