Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

93 Ađ-Đuĥaá ٱلضُّحَىٰ

< Previous   11 Āyah   The Morning Hours      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

93:1 وَٱلضُّحَىٰ
93:1 Inã rantsuwa da hantsi. - Abubakar Gumi (Hausa)

93:2 وَٱلَّيْلِ إِذَا سَجَىٰ
93:2 Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa). - Abubakar Gumi (Hausa)

93:3 مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ
93:3 Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba. - Abubakar Gumi (Hausa)

93:4 وَلَلْـَٔاخِرَةُ خَيْرٌ لَّكَ مِنَ ٱلْأُولَىٰ
93:4 Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko. - Abubakar Gumi (Hausa)

93:5 وَلَسَوْفَ يُعْطِيكَ رَبُّكَ فَتَرْضَىٰٓ
93:5 Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda. - Abubakar Gumi (Hausa)

93:6 أَلَمْ يَجِدْكَ يَتِيمًا فَـَٔاوَىٰ
93:6 Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma? - Abubakar Gumi (Hausa)

93:7 وَوَجَدَكَ ضَآلًّا فَهَدَىٰ
93:7 Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai? - Abubakar Gumi (Hausa)

93:8 وَوَجَدَكَ عَآئِلًا فَأَغْنَىٰ
93:8 Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka? - Abubakar Gumi (Hausa)

93:9 فَأَمَّا ٱلْيَتِيمَ فَلَا تَقْهَرْ
93:9 Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

93:10 وَأَمَّا ٱلسَّآئِلَ فَلَا تَنْهَرْ
93:10 Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

93:11 وَأَمَّا بِنِعْمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثْ
93:11 Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya). - Abubakar Gumi (Hausa)