Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

84 Al-'Inshiqāq ٱلْإِنْشِقَاق

< Previous   25 Āyah   The Sundering      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

84:1 إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنشَقَّتْ
84:1 Idan sama ta kẽce, - Abubakar Gumi (Hausa)

84:2 وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ
84:2 Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron, - Abubakar Gumi (Hausa)

84:3 وَإِذَا ٱلْأَرْضُ مُدَّتْ
84:3 Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta, - Abubakar Gumi (Hausa)

84:4 وَأَلْقَتْ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتْ
84:4 Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:5 وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ
84:5 Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren, - Abubakar Gumi (Hausa)

84:6 يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْإِنسَـٰنُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَىٰ رَبِّكَ كَدْحًا فَمُلَـٰقِيهِ
84:6 Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:7 فَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَـٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ
84:7 To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:8 فَسَوْفَ يُحَاسَبُ حِسَابًا يَسِيرًا
84:8 To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:9 وَيَنقَلِبُ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦ مَسْرُورًا
84:9 Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:10 وَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَـٰبَهُۥ وَرَآءَ ظَهْرِهِۦ
84:10 Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:11 فَسَوْفَ يَدْعُوا۟ ثُبُورًا
84:11 To, zã shi dinga kiran halaka! - Abubakar Gumi (Hausa)

84:12 وَيَصْلَىٰ سَعِيرًا
84:12 Kuma ya shiga sa'ĩr. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:13 إِنَّهُۥ كَانَ فِىٓ أَهْلِهِۦ مَسْرُورًا
84:13 Lal1e ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:14 إِنَّهُۥ ظَنَّ أَن لَّن يَحُورَ
84:14 Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:15 بَلَىٰٓ إِنَّ رَبَّهُۥ كَانَ بِهِۦ بَصِيرًا
84:15 Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:16 فَلَآ أُقْسِمُ بِٱلشَّفَقِ
84:16 To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:17 وَٱلَّيْلِ وَمَا وَسَقَ
84:17 Da dare, da abin da ya ƙunsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:18 وَٱلْقَمَرِ إِذَا ٱتَّسَقَ
84:18 Da watã idan (haskensa) ya cika. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:19 لَتَرْكَبُنَّ طَبَقًا عَن طَبَقٍ
84:19 Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:20 فَمَا لَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ
84:20 To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni? - Abubakar Gumi (Hausa)

84:21 وَإِذَا قُرِئَ عَلَيْهِمُ ٱلْقُرْءَانُ لَا يَسْجُدُونَ ۩
84:21 Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u? - Abubakar Gumi (Hausa)

84:22 بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ يُكَذِّبُونَ
84:22 Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:23 وَٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُوعُونَ
84:23 Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:24 فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ
84:24 Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)

84:25 إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ لَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍۭ
84:25 Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)