Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

68 Al-Qalam ٱلْقَلَم

< Previous   52 Āyah   The Pen      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

68:1 نٓ ۚ وَٱلْقَلَمِ وَمَا يَسْطُرُونَ
68:1 Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:2 مَآ أَنتَ بِنِعْمَةِ رَبِّكَ بِمَجْنُونٍ
68:2 Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:3 وَإِنَّ لَكَ لَأَجْرًا غَيْرَ مَمْنُونٍ
68:3 Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:4 وَإِنَّكَ لَعَلَىٰ خُلُقٍ عَظِيمٍ
68:4 Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:5 فَسَتُبْصِرُ وَيُبْصِرُونَ
68:5 Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:6 بِأَييِّكُمُ ٱلْمَفْتُونُ
68:6 Ga wanenku haukã take. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:7 إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ
68:7 Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:8 فَلَا تُطِعِ ٱلْمُكَذِّبِينَ
68:8 Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:9 وَدُّوا۟ لَوْ تُدْهِنُ فَيُدْهِنُونَ
68:9 Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:10 وَلَا تُطِعْ كُلَّ حَلَّافٍ مَّهِينٍ
68:10 Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:11 هَمَّازٍ مَّشَّآءٍۭ بِنَمِيمٍ
68:11 Mai zunɗe, mai yãwo da gulma. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:12 مَّنَّاعٍ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ
68:12 Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:13 عُتُلٍّۭ بَعْدَ ذَٰلِكَ زَنِيمٍ
68:13 Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri). - Abubakar Gumi (Hausa)

68:14 أَن كَانَ ذَا مَالٍ وَبَنِينَ
68:14 Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:15 إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ ءَايَـٰتُنَا قَالَ أَسَـٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ
68:15 Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

68:16 سَنَسِمُهُۥ عَلَى ٱلْخُرْطُومِ
68:16 Zã Mu yi masa alãma a kan hanci. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:17 إِنَّا بَلَوْنَـٰهُمْ كَمَا بَلَوْنَآ أَصْحَـٰبَ ٱلْجَنَّةِ إِذْ أَقْسَمُوا۟ لَيَصْرِمُنَّهَا مُصْبِحِينَ
68:17 Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:18 وَلَا يَسْتَثْنُونَ
68:18 Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:19 فَطَافَ عَلَيْهَا طَآئِفٌ مِّن رَّبِّكَ وَهُمْ نَآئِمُونَ
68:19 Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:20 فَأَصْبَحَتْ كَٱلصَّرِيمِ
68:20 Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:21 فَتَنَادَوْا۟ مُصْبِحِينَ
68:21 Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:22 أَنِ ٱغْدُوا۟ عَلَىٰ حَرْثِكُمْ إِن كُنتُمْ صَـٰرِمِينَ
68:22 Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:23 فَٱنطَلَقُوا۟ وَهُمْ يَتَخَـٰفَتُونَ
68:23 Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa). - Abubakar Gumi (Hausa)

68:24 أَن لَّا يَدْخُلَنَّهَا ٱلْيَوْمَ عَلَيْكُم مِّسْكِينٌ
68:24 "Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!" - Abubakar Gumi (Hausa)

68:25 وَغَدَوْا۟ عَلَىٰ حَرْدٍ قَـٰدِرِينَ
68:25 Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:26 فَلَمَّا رَأَوْهَا قَالُوٓا۟ إِنَّا لَضَآلُّونَ
68:26 Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!" - Abubakar Gumi (Hausa)

68:27 بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ
68:27 "Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

68:28 قَالَ أَوْسَطُهُمْ أَلَمْ أَقُل لَّكُمْ لَوْلَا تُسَبِّحُونَ
68:28 Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?" - Abubakar Gumi (Hausa)

68:29 قَالُوا۟ سُبْحَـٰنَ رَبِّنَآ إِنَّا كُنَّا ظَـٰلِمِينَ
68:29 Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai." - Abubakar Gumi (Hausa)

68:30 فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَلَـٰوَمُونَ
68:30 Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:31 قَالُوا۟ يَـٰوَيْلَنَآ إِنَّا كُنَّا طَـٰغِينَ
68:31 Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka." - Abubakar Gumi (Hausa)

68:32 عَسَىٰ رَبُّنَآ أَن يُبْدِلَنَا خَيْرًا مِّنْهَآ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا رَٰغِبُونَ
68:32 "Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

68:33 كَذَٰلِكَ ٱلْعَذَابُ ۖ وَلَعَذَابُ ٱلْـَٔاخِرَةِ أَكْبَرُ ۚ لَوْ كَانُوا۟ يَعْلَمُونَ
68:33 Haka dai azãbar take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:34 إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ عِندَ رَبِّهِمْ جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ
68:34 Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:35 أَفَنَجْعَلُ ٱلْمُسْلِمِينَ كَٱلْمُجْرِمِينَ
68:35 Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi? - Abubakar Gumi (Hausa)

68:36 مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ
68:36 Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)? - Abubakar Gumi (Hausa)

68:37 أَمْ لَكُمْ كِتَـٰبٌ فِيهِ تَدْرُسُونَ
68:37 Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

68:38 إِنَّ لَكُمْ فِيهِ لَمَا تَخَيَّرُونَ
68:38 Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa? - Abubakar Gumi (Hausa)

68:39 أَمْ لَكُمْ أَيْمَـٰنٌ عَلَيْنَا بَـٰلِغَةٌ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۙ إِنَّ لَكُمْ لَمَا تَحْكُمُونَ
68:39 Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kanMu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku? - Abubakar Gumi (Hausa)

68:40 سَلْهُمْ أَيُّهُم بِذَٰلِكَ زَعِيمٌ
68:40 Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)? - Abubakar Gumi (Hausa)

68:41 أَمْ لَهُمْ شُرَكَآءُ فَلْيَأْتُوا۟ بِشُرَكَآئِهِمْ إِن كَانُوا۟ صَـٰدِقِينَ
68:41 Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:42 يَوْمَ يُكْشَفُ عَن سَاقٍ وَيُدْعَوْنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ فَلَا يَسْتَطِيعُونَ
68:42 Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujũda, sai bã zã su iyãwa ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:43 خَـٰشِعَةً أَبْصَـٰرُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ ۖ وَقَدْ كَانُوا۟ يُدْعَوْنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ وَهُمْ سَـٰلِمُونَ
68:43 Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi). - Abubakar Gumi (Hausa)

68:44 فَذَرْنِى وَمَن يُكَذِّبُ بِهَـٰذَا ٱلْحَدِيثِ ۖ سَنَسْتَدْرِجُهُم مِّنْ حَيْثُ لَا يَعْلَمُونَ
68:44 Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:45 وَأُمْلِى لَهُمْ ۚ إِنَّ كَيْدِى مَتِينٌ
68:45 Ina jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:46 أَمْ تَسْـَٔلُهُمْ أَجْرًا فَهُم مِّن مَّغْرَمٍ مُّثْقَلُونَ
68:46 Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu? - Abubakar Gumi (Hausa)

68:47 أَمْ عِندَهُمُ ٱلْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَ
68:47 Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne? - Abubakar Gumi (Hausa)

68:48 فَٱصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ وَلَا تَكُن كَصَاحِبِ ٱلْحُوتِ إِذْ نَادَىٰ وَهُوَ مَكْظُومٌ
68:48 Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:49 لَّوْلَآ أَن تَدَٰرَكَهُۥ نِعْمَةٌ مِّن رَّبِّهِۦ لَنُبِذَ بِٱلْعَرَآءِ وَهُوَ مَذْمُومٌ
68:49 Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:50 فَٱجْتَبَـٰهُ رَبُّهُۥ فَجَعَلَهُۥ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
68:50 Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki. - Abubakar Gumi (Hausa)

68:51 وَإِن يَكَادُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَيُزْلِقُونَكَ بِأَبْصَـٰرِهِمْ لَمَّا سَمِعُوا۟ ٱلذِّكْرَ وَيَقُولُونَ إِنَّهُۥ لَمَجْنُونٌ
68:51 Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!" - Abubakar Gumi (Hausa)

68:52 وَمَا هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَـٰلَمِينَ
68:52 Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya. - Abubakar Gumi (Hausa)