Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

92 Al-Layl ٱللَّيْل

< Previous   21 Āyah   The Night      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

92:1 وَٱلَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰ
92:1 Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:2 وَٱلنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ
92:2 Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:3 وَمَا خَلَقَ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰٓ
92:3 Da abin da ya halitta namiji da mace. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:4 إِنَّ سَعْيَكُمْ لَشَتَّىٰ
92:4 Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:5 فَأَمَّا مَنْ أَعْطَىٰ وَٱتَّقَىٰ
92:5 To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:6 وَصَدَّقَ بِٱلْحُسْنَىٰ
92:6 Kuma ya gaskata kalma mai kyãwo. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:7 فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلْيُسْرَىٰ
92:7 To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:8 وَأَمَّا مَنۢ بَخِلَ وَٱسْتَغْنَىٰ
92:8 Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:9 وَكَذَّبَ بِٱلْحُسْنَىٰ
92:9 Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:10 فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلْعُسْرَىٰ
92:10 To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:11 وَمَا يُغْنِى عَنْهُ مَالُهُۥٓ إِذَا تَرَدَّىٰٓ
92:11 Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta). - Abubakar Gumi (Hausa)

92:12 إِنَّ عَلَيْنَا لَلْهُدَىٰ
92:12 Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:13 وَإِنَّ لَنَا لَلْـَٔاخِرَةَ وَٱلْأُولَىٰ
92:13 Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:14 فَأَنذَرْتُكُمْ نَارًا تَلَظَّىٰ
92:14 Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:15 لَا يَصْلَىٰهَآ إِلَّا ٱلْأَشْقَى
92:15 Bãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:16 ٱلَّذِى كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
92:16 Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:17 وَسَيُجَنَّبُهَا ٱلْأَتْقَى
92:17 Kuma mafi taƙawa zai nisance ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:18 ٱلَّذِى يُؤْتِى مَالَهُۥ يَتَزَكَّىٰ
92:18 Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:19 وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُۥ مِن نِّعْمَةٍ تُجْزَىٰٓ
92:19 Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:20 إِلَّا ٱبْتِغَآءَ وَجْهِ رَبِّهِ ٱلْأَعْلَىٰ
92:20 Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

92:21 وَلَسَوْفَ يَرْضَىٰ
92:21 To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi). - Abubakar Gumi (Hausa)