Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

91 Ash-Shams ٱلشَّمْس

< Previous   15 Āyah   The Sun      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

91:1 وَٱلشَّمْسِ وَضُحَىٰهَا
91:1 Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta. - Abubakar Gumi (Hausa)

91:2 وَٱلْقَمَرِ إِذَا تَلَىٰهَا
91:2 Kuma da wata idan ya bi ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

91:3 وَٱلنَّهَارِ إِذَا جَلَّىٰهَا
91:3 Da yini a lõkacin da ya bayyana ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

91:4 وَٱلَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰهَا
91:4 Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

91:5 وَٱلسَّمَآءِ وَمَا بَنَىٰهَا
91:5 Da sama da abin da ya gina ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

91:6 وَٱلْأَرْضِ وَمَا طَحَىٰهَا
91:6 Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

91:7 وَنَفْسٍ وَمَا سَوَّىٰهَا
91:7 Da rai da abin da ya daidaita shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

91:8 فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَىٰهَا
91:8 Sa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

91:9 قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّىٰهَا
91:9 Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo. - Abubakar Gumi (Hausa)

91:10 وَقَدْ خَابَ مَن دَسَّىٰهَا
91:10 Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe. - Abubakar Gumi (Hausa)

91:11 كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِطَغْوَىٰهَآ
91:11 Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu. - Abubakar Gumi (Hausa)

91:12 إِذِ ٱنۢبَعَثَ أَشْقَىٰهَا
91:12 A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu). - Abubakar Gumi (Hausa)

91:13 فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ ٱللَّهِ نَاقَةَ ٱللَّهِ وَسُقْيَـٰهَا
91:13 Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!" - Abubakar Gumi (Hausa)

91:14 فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمْدَمَ عَلَيْهِمْ رَبُّهُم بِذَنۢبِهِمْ فَسَوَّىٰهَا
91:14 Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi). - Abubakar Gumi (Hausa)

91:15 وَلَا يَخَافُ عُقْبَـٰهَا
91:15 Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar). - Abubakar Gumi (Hausa)