Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

104 Al-Humazah ٱلْهُمَزَة

< Previous   9 Āyah   The Traducer      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

104:1 وَيْلٌ لِّكُلِّ هُمَزَةٍ لُّمَزَةٍ
104:1 Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa). - Abubakar Gumi (Hausa)

104:2 ٱلَّذِى جَمَعَ مَالًا وَعَدَّدَهُۥ
104:2 Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

104:3 يَحْسَبُ أَنَّ مَالَهُۥٓ أَخْلَدَهُۥ
104:3 Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

104:4 كَلَّا ۖ لَيُنۢبَذَنَّ فِى ٱلْحُطَمَةِ
104:4 A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama. - Abubakar Gumi (Hausa)

104:5 وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْحُطَمَةُ
104:5 Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama? - Abubakar Gumi (Hausa)

104:6 نَارُ ٱللَّهِ ٱلْمُوقَدَةُ
104:6 Wutar Allah ce wadda ake hurawa. - Abubakar Gumi (Hausa)

104:7 ٱلَّتِى تَطَّلِعُ عَلَى ٱلْأَفْـِٔدَةِ
104:7 Wadda take lẽƙãwa a kan zukata. - Abubakar Gumi (Hausa)

104:8 إِنَّهَا عَلَيْهِم مُّؤْصَدَةٌ
104:8 Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu. - Abubakar Gumi (Hausa)

104:9 فِى عَمَدٍ مُّمَدَّدَةٍۭ
104:9 A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu. - Abubakar Gumi (Hausa)