Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

100 Al-`Ādiyāt ٱلْعَادِيَات

< Previous   11 Āyah   The Courser      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

100:1 وَٱلْعَـٰدِيَـٰتِ ضَبْحًا
100:1 Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki. - Abubakar Gumi (Hausa)

100:2 فَٱلْمُورِيَـٰتِ قَدْحًا
100:2 Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa. - Abubakar Gumi (Hausa)

100:3 فَٱلْمُغِيرَٰتِ صُبْحًا
100:3 Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba. - Abubakar Gumi (Hausa)

100:4 فَأَثَرْنَ بِهِۦ نَقْعًا
100:4 Sai su motsar da ƙũra game da shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

100:5 فَوَسَطْنَ بِهِۦ جَمْعًا
100:5 Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

100:6 إِنَّ ٱلْإِنسَـٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودٌ
100:6 Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

100:7 وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٌ
100:7 Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka. - Abubakar Gumi (Hausa)

100:8 وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلْخَيْرِ لَشَدِيدٌ
100:8 Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

100:9 ۞ أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِى ٱلْقُبُورِ
100:9 Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura. - Abubakar Gumi (Hausa)

100:10 وَحُصِّلَ مَا فِى ٱلصُّدُورِ
100:10 Aka bayyana abin da ke cikin zukata. - Abubakar Gumi (Hausa)

100:11 إِنَّ رَبَّهُم بِهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّخَبِيرٌۢ
100:11 Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne? - Abubakar Gumi (Hausa)