Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

82 Al-'Infiţār ٱلْإِنْفِطَار

< Previous   19 Āyah   The Cleaving      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

82:1 إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتْ
82:1 Idan sama ta tsãge. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:2 وَإِذَا ٱلْكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتْ
82:2 Kuma idan taurãri suka wãtse. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:3 وَإِذَا ٱلْبِحَارُ فُجِّرَتْ
82:3 Kuma idan tẽkuna aka facce su. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:4 وَإِذَا ٱلْقُبُورُ بُعْثِرَتْ
82:4 Kuma idan kaburbura aka tõne su. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:5 عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ
82:5 Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:6 يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْإِنسَـٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلْكَرِيمِ
82:6 Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:7 ٱلَّذِى خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ
82:7 Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:8 فِىٓ أَىِّ صُورَةٍ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ
82:8 A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:9 كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ
82:9 A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako! - Abubakar Gumi (Hausa)

82:10 وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَـٰفِظِينَ
82:10 Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:11 كِرَامًا كَـٰتِبِينَ
82:11 Mãsu daraja, marubũta. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:12 يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ
82:12 Sunã sanin abin da kuke aikatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:13 إِنَّ ٱلْأَبْرَارَ لَفِى نَعِيمٍ
82:13 Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:14 وَإِنَّ ٱلْفُجَّارَ لَفِى جَحِيمٍ
82:14 Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:15 يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ ٱلدِّينِ
82:15 Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:16 وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَآئِبِينَ
82:16 Bã zã su faku daga gare ta ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

82:17 وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ
82:17 Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako? - Abubakar Gumi (Hausa)

82:18 ثُمَّ مَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ
82:18 Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako? - Abubakar Gumi (Hausa)

82:19 يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِّنَفْسٍ شَيْـًٔا ۖ وَٱلْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِّلَّهِ
82:19 Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake. - Abubakar Gumi (Hausa)