Selected
                        Original Text
                        
                    
                
                    
                        Abubakar Gumi
                        
                        
                        
                    
                
                Abdullah Yusuf Ali
Abdul Majid Daryabadi
Abul Ala Maududi
Ahmed Ali
Ahmed Raza Khan
A. J. Arberry
Ali Quli Qarai
Hasan al-Fatih Qaribullah and Ahmad Darwish
Mohammad Habib Shakir
Mohammed Marmaduke William Pickthall
Muhammad Sarwar
Muhammad Taqi-ud-Din al-Hilali and Muhammad Muhsin Khan
Safi-ur-Rahman al-Mubarakpuri
Saheeh International
Talal Itani
Transliteration
Wahiduddin Khan
                    بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
                
                
                    In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.
                
            
                    82:1
                    إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتْ
                
                
                
                
                
                    82:1
                    Idan sama ta tsãge.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:2
                    وَإِذَا ٱلْكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتْ
                
                
                
                
                
                    82:2
                    Kuma idan taurãri suka wãtse.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:3
                    وَإِذَا ٱلْبِحَارُ فُجِّرَتْ
                
                
                
                
                
                    82:3
                    Kuma idan tẽkuna aka facce su.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:4
                    وَإِذَا ٱلْقُبُورُ بُعْثِرَتْ
                
                
                
                
                
                    82:4
                    Kuma idan kaburbura aka tõne su.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:5
                    عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ
                
                
                
                
                
                    82:5
                    Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:6
                    يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْإِنسَـٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلْكَرِيمِ
                
                
                
                
                
                    82:6
                    Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:7
                    ٱلَّذِى خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ
                
                
                
                
                
                    82:7
                    Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:8
                    فِىٓ أَىِّ صُورَةٍ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ
                
                
                
                
                
                    82:8
                    A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:9
                    كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ
                
                
                
                
                
                    82:9
                    A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:10
                    وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَـٰفِظِينَ
                
                
                
                
                
                    82:10
                    Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:11
                    كِرَامًا كَـٰتِبِينَ
                
                
                
                
                
                    82:11
                    Mãsu daraja, marubũta.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:12
                    يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ
                
                
                
                
                
                    82:12
                    Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:13
                    إِنَّ ٱلْأَبْرَارَ لَفِى نَعِيمٍ
                
                
                
                
                
                    82:13
                    Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:14
                    وَإِنَّ ٱلْفُجَّارَ لَفِى جَحِيمٍ
                
                
                
                
                
                    82:14
                    Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:15
                    يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ ٱلدِّينِ
                
                
                
                
                
                    82:15
                    Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:16
                    وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَآئِبِينَ
                
                
                
                
                
                    82:16
                    Bã zã su faku daga gare ta ba.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:17
                    وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ
                
                
                
                
                
                    82:17
                    Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:18
                    ثُمَّ مَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ
                
                
                
                
                
                    82:18
                    Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    82:19
                    يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِّنَفْسٍ شَيْـًٔا ۖ وَٱلْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِّلَّهِ
                
                
                
                
                
                    82:19
                    Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.  - Abubakar Gumi (Hausa)