Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

60 Al-Mumtaĥanah ٱلْمُمْتَحَنَة

< Previous   13 Āyah   She that is to be examined      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

60:10 يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِذَا جَآءَكُمُ ٱلْمُؤْمِنَـٰتُ مُهَـٰجِرَٰتٍ فَٱمْتَحِنُوهُنَّ ۖ ٱللَّهُ أَعْلَمُ بِإِيمَـٰنِهِنَّ ۖ فَإِنْ عَلِمْتُمُوهُنَّ مُؤْمِنَـٰتٍ فَلَا تَرْجِعُوهُنَّ إِلَى ٱلْكُفَّارِ ۖ لَا هُنَّ حِلٌّ لَّهُمْ وَلَا هُمْ يَحِلُّونَ لَهُنَّ ۖ وَءَاتُوهُم مَّآ أَنفَقُوا۟ ۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ أَن تَنكِحُوهُنَّ إِذَآ ءَاتَيْتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ ۚ وَلَا تُمْسِكُوا۟ بِعِصَمِ ٱلْكَوَافِرِ وَسْـَٔلُوا۟ مَآ أَنفَقْتُمْ وَلْيَسْـَٔلُوا۟ مَآ أَنفَقُوا۟ ۚ ذَٰلِكُمْ حُكْمُ ٱللَّهِ ۖ يَحْكُمُ بَيْنَكُمْ ۚ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
60:10 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan mãtã mũminai suka zo muku, sunã mãsu hijira, to, ku jarraba su. Allah Shĩ ne mafi sani ga ĩmãninsu. To, idan kun san sũ mũminai ne, kada ku mayar da su zuwa ga kãfirai. Sũ mãtan bã su halatta ga aurensu, sũ kuma kãfiran bã su halatta ga auren mãtan. Ku bã su abin da suka ɓatar na dũkiya. Kuma bãbu laifi a kanku ga ku aure su idan kun bã su sadãkõkinsu. Kuma kada ku riƙe auren mãtã kãfirai, kuma ku tambayi abin da kuka ɓatar daga dũkiya, su kuma kãfirai su tambayi abin da suka ɓatar na dũkiya. Wannan hukuncin Allah ne Yanã hukunci a tsakãninku. kuma Allah, Masani ne, Mai hikima - Abubakar Gumi (Hausa)