Selected
                        Original Text
                        
                    
                
                    
                        Abubakar Gumi
                        
                        
                        
                    
                
                Abdullah Yusuf Ali
Abdul Majid Daryabadi
Abul Ala Maududi
Ahmed Ali
Ahmed Raza Khan
A. J. Arberry
Ali Quli Qarai
Hasan al-Fatih Qaribullah and Ahmad Darwish
Mohammad Habib Shakir
Mohammed Marmaduke William Pickthall
Muhammad Sarwar
Muhammad Taqi-ud-Din al-Hilali and Muhammad Muhsin Khan
Safi-ur-Rahman al-Mubarakpuri
Saheeh International
Talal Itani
Transliteration
Wahiduddin Khan
                    بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
                
                
                    In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.
                
            
                    78:1
                    عَمَّ يَتَسَآءَلُونَ
                
                
                
                
                
                    78:1
                    A kan mẽ suke tambayar jũna?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:2
                    عَنِ ٱلنَّبَإِ ٱلْعَظِيمِ
                
                
                
                
                
                    78:2
                    A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:3
                    ٱلَّذِى هُمْ فِيهِ مُخْتَلِفُونَ
                
                
                
                
                
                    78:3
                    Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:4
                    كَلَّا سَيَعْلَمُونَ
                
                
                
                
                
                    78:4
                    A'aha! Zã su sani.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:5
                    ثُمَّ كَلَّا سَيَعْلَمُونَ
                
                
                
                
                
                    78:5
                    Kuma, a'aha! Zã su sani.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:6
                    أَلَمْ نَجْعَلِ ٱلْأَرْضَ مِهَـٰدًا
                
                
                
                
                
                    78:6
                    Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:7
                    وَٱلْجِبَالَ أَوْتَادًا
                
                
                
                
                
                    78:7
                    Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:8
                    وَخَلَقْنَـٰكُمْ أَزْوَٰجًا
                
                
                
                
                
                    78:8
                    Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:9
                    وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًا
                
                
                
                
                
                    78:9
                    Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:10
                    وَجَعَلْنَا ٱلَّيْلَ لِبَاسًا
                
                
                
                
                
                    78:10
                    Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:11
                    وَجَعَلْنَا ٱلنَّهَارَ مَعَاشًا
                
                
                
                
                
                    78:11
                    Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:12
                    وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًا
                
                
                
                
                
                    78:12
                    Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:13
                    وَجَعَلْنَا سِرَاجًا وَهَّاجًا
                
                
                
                
                
                    78:13
                    Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:14
                    وَأَنزَلْنَا مِنَ ٱلْمُعْصِرَٰتِ مَآءً ثَجَّاجًا
                
                
                
                
                
                    78:14
                    Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:15
                    لِّنُخْرِجَ بِهِۦ حَبًّا وَنَبَاتًا
                
                
                
                
                
                    78:15
                    Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:16
                    وَجَنَّـٰتٍ أَلْفَافًا
                
                
                
                
                
                    78:16
                    Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:17
                    إِنَّ يَوْمَ ٱلْفَصْلِ كَانَ مِيقَـٰتًا
                
                
                
                
                
                    78:17
                    Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:18
                    يَوْمَ يُنفَخُ فِى ٱلصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًا
                
                
                
                
                
                    78:18
                    Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:19
                    وَفُتِحَتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتْ أَبْوَٰبًا
                
                
                
                
                
                    78:19
                    Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:20
                    وَسُيِّرَتِ ٱلْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًا
                
                
                
                
                
                    78:20
                    Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:21
                    إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتْ مِرْصَادًا
                
                
                
                
                
                    78:21
                    Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:22
                    لِّلطَّـٰغِينَ مَـَٔابًا
                
                
                
                
                
                    78:22
                    Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:23
                    لَّـٰبِثِينَ فِيهَآ أَحْقَابًا
                
                
                
                
                
                    78:23
                    Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:24
                    لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًا
                
                
                
                
                
                    78:24
                    Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:25
                    إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًا
                
                
                
                
                
                    78:25
                    Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:26
                    جَزَآءً وِفَاقًا
                
                
                
                
                
                    78:26
                    Sakamako mai dãcẽwa.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:27
                    إِنَّهُمْ كَانُوا۟ لَا يَرْجُونَ حِسَابًا
                
                
                
                
                
                    78:27
                    Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:28
                    وَكَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا كِذَّابًا
                
                
                
                
                
                    78:28
                    Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa!  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:29
                    وَكُلَّ شَىْءٍ أَحْصَيْنَـٰهُ كِتَـٰبًا
                
                
                
                
                
                    78:29
                    Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:30
                    فَذُوقُوا۟ فَلَن نَّزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًا
                
                
                
                
                
                    78:30
                    Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:31
                    إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًا
                
                
                
                
                
                    78:31
                    Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:32
                    حَدَآئِقَ وَأَعْنَـٰبًا
                
                
                
                
                
                    78:32
                    Lambuna da inabõbi.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:33
                    وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًا
                
                
                
                
                
                    78:33
                    Da cikakkun 'yammata, tsãrar jũna.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:34
                    وَكَأْسًا دِهَاقًا
                
                
                
                
                
                    78:34
                    Da hinjãlan giya cikakku.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:35
                    لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّٰبًا
                
                
                
                
                
                    78:35
                    Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:36
                    جَزَآءً مِّن رَّبِّكَ عَطَآءً حِسَابًا
                
                
                
                
                
                    78:36
                    Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:37
                    رَّبِّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ٱلرَّحْمَـٰنِ ۖ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًا
                
                
                
                
                
                    78:37
                    Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:38
                    يَوْمَ يَقُومُ ٱلرُّوحُ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ صَفًّا ۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحْمَـٰنُ وَقَالَ صَوَابًا
                
                
                
                
                
                    78:38
                    Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:39
                    ذَٰلِكَ ٱلْيَوْمُ ٱلْحَقُّ ۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ مَـَٔابًا
                
                
                
                
                
                    78:39
                    Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.  - Abubakar Gumi (Hausa)
                
                
                
                
                
                    78:40
                    إِنَّآ أَنذَرْنَـٰكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ ٱلْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ ٱلْكَافِرُ يَـٰلَيْتَنِى كُنتُ تُرَٰبًۢا
                
                
                
                
                
                    78:40
                    Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"  - Abubakar Gumi (Hausa)