Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

4 An-Nisā' ٱلنِّسَاء

< Previous   176 Āyah   The Women      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

4:46 مِّنَ ٱلَّذِينَ هَادُوا۟ يُحَرِّفُونَ ٱلْكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِۦ وَيَقُولُونَ سَمِعْنَا وَعَصَيْنَا وَٱسْمَعْ غَيْرَ مُسْمَعٍ وَرَٰعِنَا لَيًّۢا بِأَلْسِنَتِهِمْ وَطَعْنًا فِى ٱلدِّينِ ۚ وَلَوْ أَنَّهُمْ قَالُوا۟ سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا وَٱسْمَعْ وَٱنظُرْنَا لَكَانَ خَيْرًا لَّهُمْ وَأَقْوَمَ وَلَـٰكِن لَّعَنَهُمُ ٱللَّهُ بِكُفْرِهِمْ فَلَا يُؤْمِنُونَ إِلَّا قَلِيلًا
4:46 Daga waɗanda suka tũba (Yahũdu), akwai wasu sunã karkatar da magana daga wurãrenta suna cẽwa: "Munjiya kuma mun ƙiya, kuma ka jiya a wani wurin jiyãwa, kuma rã'ina (da ma'anar 'ruɓaɓɓe'), ka tsare mu," dõmin karkatarwa da harsunansu, kuma dõmin sũkã a cikin addini. Kuma dã lalle sũ, sun ce: "Mun jiya kuma mun yi ɗa'a, kuma ka saurãra kuma ka dãkata mana," haƙĩƙa, dã ya kasance mafi alhẽri a gare su, kuma mafi daidaita; amma Allah Yã la'anẽ su, sabõda kãfircinsu don haka bã zã su yi ĩmãni ba, sai kaɗan. - Abubakar Gumi (Hausa)